Shugaba Buhari ya ce, nan kusa 'yan Najeriya za su fara ganin tasirin canjin da suka zaba a dukkanin sassan kasar.
Wata sanarwa da fadar Buhari ta fitar ta ce, gwamnatin tarayya ta yi asarar Naira tiriliyan 9 saboda rikicin Boko Haram, abinda da ya kara tsananta matsalar tattalin arzikin da kasar ke ciki.
Gwamnatin Najeriya ta sanar da jerin shirye-shiryenta don inganta rayuwar al’umma, da suka hada da shirin bai wa marasa galihu tallafin Naira dubu 5 a duk karshen wata, wanda ta ce, nan kusa za a fara aiwatarwa.
Gwamnatin dai na bukatar ‘yan Najeriya su fahimci cewa, ta gaji tarin matsaloli daga tsohuwar gwamnatin da ta shude.288